Shugaban Gidan rediyon jihar Kano Kwamared Abubakar Adamu Rano ya ce yana mamakin yadda wasu daga cikin Shugabannin jam’iyyar APC su ke cewa za su karbi Kano a zaben shekara ta 2024.
” Al’ummar jihar Kano dai aiki su ke so , kuma shi ne dalilin da yasa su ka zabi Abba Kabir Yusuf kuma yana yi musu to ta yaya al’ummar jihar Kano za su ajiye gwamnatinmu da muke yi musu abun da su ka zabe mu saboda shi su dawo da jam’iyyar APC”.
Abubakar Adamu Rano ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa ta musamman da yayi da jaridar Kadaura24.

Shugaban Radio Kano ya ce gwamnan Abba Kabir Yusuf ya dukufa yana ta yin aiki a birnin da karkara, sannan yana taimakawa al’umma ta hanyar gina rayuwarsu to ta yaya APC ta karbi Kano a hannunsa?.
” Na yi imani ko iya aiyukan da na yi a Radio Kano daga zuwa na sun isa mu yi tawassali da su mu yiwa Abba Kabir Yusuf yakin neman zaben shekara ta 2027, kuma Ina da yakinin kanawan za su ba shi kuri’unsu”. A cewar MD Radio Kano
Yanzu-yanzu: Jam’iyyar APC ta Fadi Matsayarta Kan Sulhunta Kwankwaso da Ganduje
Ya ce a zamani mulkin APC Kano ta rasa damammaki da yawa, amma yanzu ruhi da martabar jihar sun dawo saboda Gwamnan yana kwatanta gaskiya da adalci sabanin lokacin da APC take mulki.
Abubakar Adamu Rano ya APC ta hakura kawai, saboda abun da suke mafarki ba mai yiwuwa ba ne, ” Da za su iya karbar mulki a wajenmu, ai da ba su bari mun kayar da su a zabukan 2019 da 2023 ba.