Daga Aisha Muhammad Adam
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya jaddada kudirinsa na aiki kafada da kafada da masu ruwa da tsaki a fannin yada labarai domin cimma manufar da ta sa aka samar da ma’aikatar.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin Shugabannin gidan jaridar Daily trust, wadanda suka je domin taya shi murnar mukamin da gwamnan Kano ya ba shi.

Yayin ziyarar Kwamared Waiya ya bayyana cewa suna da kyakykyawa kuma dadaddiyar alakar aiki tsakanin shi da Daily trust , har sai da tuna musu irin gudunmawar shawarwari da ya bayar domin bude talabijin dinsu na Trust Tv.
Ya yabawa gidan jaridar bisa irin gudunmawar da suke bayarwa wajen yada labarai da kuma kokarin da suke na an Karar da gwamnati irin nauyin al’umma dake kansu.
Waiya ya gode musu bisa ziyarar sannan ya basu tabbacin yin aiki tare domin yada manufofin gwamnatin jihar Kano dake karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf.
A nasa jawabin tun da fari, Babban jami’in kamfanin Media trust Ahmad Ibrahim Shekarau ya yabawa gwamnan Kano bisa duba chanchantar Waiya har ya nada shi a matsayin kwamishinan yada labarai.
Ya ba da tabbacin za a cigaba da kyautata alakar dake tsakaninsu da gwamnatin jihar Kano Wanda ya ce duk sati ma akwai wani shiri da suke yiwa gwamnatin a Tv, wanda ke yada manufofin gwamnatin Kanon.