Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Dakarun haɗin gwiwa na ‘Operation Hadin Kai’ a Arewa-maso-Gabas sun haramta yin amfani da jiragen sama marasa matuka, da ake kira drones, a yankin.
Kwamandan Sashen Sojan Sama, Air Commodore U. U. Idris ne ya bayar da wannan umarni a wata sanarwa da Daily Trust ta gani, inda ya ce amfani da drones ba tare da izini ba na iya haifar da barazana a jihohin Borno, Yobe, da Adamawa.
Ya koka cewa hukumomin gwamnati da kuma wasu mutane masu zaman kansu na amfani da drones ba tare da amincewar Sashen Sojan Sama na Operation Hadin Kai ba.