Tsarin Manchester United bai dace da ni ba – Zidane

Date:

Yunƙurin Manchester United na ɗauko Zinedine Zidane ya gamu da cikas, inda wasu majiyoyi na kusa da tsohon kocin Real Madrid ya ce ba ya sha’awar zuwa Old Trafford.

A ranar Asabar Manchester United ta raba gari da Ole Gunner Soskjear bayan kashin da da ƙungiyar ta sha hannuin Watford 4-1.

A watan Mayun bana Zidane a bar Real Madrid a matsayin kocinta karo na biyu.

Ya lashe kofin zakarun turai a Madrid sau uku a jere daga 2016.

Bayan ya bar ƙungiyar a 2018, ya sake dawo wa daga baya inda kuma ya lashe kofin La Liga da Super Cup a 2020.

Majiyoyin da ke kusa da tsohon ɗan wasan na Faransa sun ce Zidane wanda yanzu ba shi da ƙungiya ba ya da sha’awar aikin horar da Manchester United.

An alaƙanta shi da ƙungiyar Paris St-Germain ta Faransa, kuma zai fi maraba da buƙatar idan har ta samu.

  1. Mauricio Pochettino, wanda aka fi maganarsa a matsayin wanda zai zama kocin Manchester,yanzu shi ne mai horar da PSG kuma ana tunanin Zidane zai iya maye gurbinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...

Al’ummar Kano ku baiwa AA Zaura hadin Kai domin ya kawo karshen fadan Daba – Baba Yawale

Daga Halima Umar Dogo   Babban Hadimin AA Zaura Alhaji Baba...