Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya sanar da cewa gwamnatin jihar za ta rage farashin man fetur ga manoma a yankunan da rikicin Boko Haram ya shafa.
Zulum ya sanar da wannan tallafi ne a jiya Juma’a a garin Bama yayin da ya kaddamar da rabon kayan noma ga manoma sama da 5,000 da Boko Haram ta taba korar su daga muhallansu.
A cewar gwamnan, farashin litar man fetur da ake sayarwa tsakanin N1,000 zuwa N1,200 a Maiduguri za a sayar wa manoma kan N600.
Hukumar Tace Fina-fina ta Kano ta Dakatar da Babbar Jaruma a Kannywood
Wannan mataki, a cewar sa, na da nufin rage nauyin kudin da ke kan manoman a yankunan da su ka fuskanci lalacewar tattalin arziki da gine-gine sakamakon shekaru na rikici.