Hukumar Tace Fina-fina ta Kano ta Dakatar da Babbar Jaruma a Kannywood

Date:

Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano ta dakatar da Sahma M Inuwa daga shiga harkar film na tsawon shekara daya, tare da kwace shedarta ta zama halartacciyar yar film.

A wata sanarwar da jami’in yada labaran Hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya aikawa manema labarai ya shaida cewa Hukumar ta sha al’washin kin kara tace duk wani film da Samha ta fito a ciki.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jama’in hulda da jama’a na Hukumar Abdullahi sani Sulaiman ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Kano.

Wannan ya biyoya wasu korafe korafe da al’umma sukayi kan wani bidiyo da jarumar ta saki dake nuna shigar da bata dace da koyarwar addinin musulunci ba, baya ga samunta da yin kalaman da basu dace ba.

Ya zuwa yanzu dai Hukumar ta dakatar da Samha har tsawon shekara daya a wani mataki na tabbatar da bin dokokin Hukumar tare da kara tsaftace Masana’antar kannywood.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa Hukumar ta ce tana daukar irin wadannan matakan ne domin tsaftace harkar fina-finan Kannywood

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...