Shugaban hukumar raya kogunan Hadejia – Jama’are Engr. Rabi’u Sulaiman Bichi ya bayyana wasu kudirori da yake son aikawatarwa da zarar ya fara aiki a hukumar domin ciyar da jihohin Kano Jigawa da Bauchi gaba ta fuskar aikin noma.
” Duk da dai ban shiga Ofis ba, amma na gudanar da bincike kuma na tsara wasu kudirori kusan guda 3 zuwa 4 da nake son aiwatar da su, domin ganin Mun dawo da martabar harkokin noma kamar yadda shugaban ƙasa Bola Tinubu yake fata”.
Rabi’u Sulaiman Bichi ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da wakilin jaridar kadaura24 a Kano.
Sabon Shugaban hukumar ya ce zai zo da tsarin da zai ba da damar inganta takin gargajiya da ake amfani da shi, ta yadda zai zama yana yiwa manoma aiki yadda ya kamata, ba kamar yadda ake amfani da shi a baya ba.
” Batun irin za mu yi kokari mu ga Mun samar da ingantaccen irin wanda zai taimaka manoma su sami amfani mai kyau kuma mai yawa, domin akwai irin shuka kala-kala da ake da shi , musamman a kasashen da suka ci gaba to zamu samar da hanyoyin da manoma za su rika samun iri mai kyau kuma cikin sauki”. Inji MD Hadejia – Jama’are
Bayan NNPCL ya gyara matatar mai ta Warri, Tinubu ya yabawa kamfanin
Ya ce zai tabbatar da cusa son harkokin noma a zukatan Matasan jihohin Kano Jigawa da Bauchi, ta hanyar koya musu harkokin noma da kuma tabbatar da sun sami tallafin da ya dace daga hukumomin da suka chanchanta.
Sabon Shugaban hukumar ta raya kogunan Hadejia – Jama’are akwai damammaki masu yawa da ya kamata manoma su rika amfana da su amma ba sa samu Saboda wasu matsaloli, Amma ya ba da tabbacin yin duk mai yiwuwa don ganin manoman wannan jihohin sun amfana.