Har yanzu dai manyan zarge zargen nan da shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdulrahman Thiani ya yi wa shugabannin Najeriya, na taimaka wa yan ta’adda, da kuma ba wa sojojin Faransa matsuguni a yankin tafkin Chadi, na ci gaba da tayar da ƙura, inda a wannan karon, al’ummomin da ke zaune a yankin suka fara tofa albarkacin bakinsu a kan batun.
Domin tabbatar da ko akwai ƙanshin gaskiya a zargin na shugaban mulkin sojin na Nijar, sashen Hausa na BBC ya tuntubi wasu mazauna yankin da ke rayuwa a cikinsa a kullu-yaumin.
Alhaji Abubakar Gamandi, shugaban masu kamun kifi na tafkin Chadi, ya ce a iya saninn su ba alamun wasu baƙin fuskoki daga waje da suka kafa wani sansani ko suke kai-kawo a garuruwan da shugaban na Nijar ya ambata, ko wani sashe na yankin tafkin Chadin baki ɗaya.
”Kamar Kangarwan da yake maganar an kawo jami’an tsaro an ajiye, to a gaskiya yanzu wannan wuri ya zama kufai, babu kowa a cikinsa, sanadiyyar yaƙin Boko Haram, garin ya tarwatse kowa ya fice, sojojin Najeriya da na Chadi ne kawai suke aiki a wannan gari, babu wani ɗan adam a cikinsa in ba waɗannan jami’an tsaro ba” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ”kamar Kurnawa da ke kusa da Nijar ɗin da shugaba Tchiani ya ambata, nan ma babu wata baƙuwar fuska a wurin, in ba mayakan Boko Haram da ke rayuwa tare da wasu tsirarun Fulani ba, waɗanda dama tun asali a nan suke rayuwa”.
”Kuma na ji shi shugaban mulkin sojin Nijar na maganar wani waje da aka sa masa sunan Canada, babu wannan wuri a duk tsibirin tafkin Chadi, tun daga ɓangaren Najeriya da na Chadi da kuma Nijar ɗin da kuma Kamaru, mun san wannan wuri gaba-da-baya, kuma babu wannan wuri” inji shi.
Abubakar Sabo na Dala Radio ya sami Sabon Mukami
Sai dai da sashen Hausa na BBC ya tambaye shi ko baya ganin wataƙila tun da lamari ne na tsaro an suturta wajen ne saboda kada jama’a su sani ?, sai ya ce ”Ai ko aljani da yake tafkin Chadi ya san mun san wannan yanki, babu wani abu da zai faru da za a ce bamu san shi ba, ba zai taɓa yiwuwa ba, idan ma wasu ne suka ba wa shugaba Tchiani labari to gaskiya akwai kuskure a abun da aka faɗa masa” inji Alhaji Abubakar Gamandi, shugaban masu sana’ar kamun kifi na yankin na tafkin Chadi.
Dama dai Najeriya ta musanta zarge zargen na shugaban mulkin sojin Nijar, domin ko a wata hira da muka yi da mai ba wa shugaban ƙasar shawara kan sha’anin tsaro Nuhu Ribaɗu, ya ce zarge zargen basu da tushe ballantana makama, inda ya ƙalubalanci mu kanmu ƴan jarida da mu bincika wuraren da shugaban ya faɗa mu gani, lamarin da ya sa sashen Hausa na BBC ya amsa wannan ƙalubale.
Wannan al’amari dai na ci gaba da tayar da ƙura musamman a Najeriya, inda mutane da dama ke ganin cewa babu abun da hakan zai haifar, face ƙara bata dangantakar da ke akwai tsakanin daɗaɗɗun kawayen biyu, na tun fil-azal, da mutanensu, da al’adunsu, da kuma addinansu suka zo ɗaya.
Tun lokacin da sojoji ƙarƙashin jagorancin Janar Abdulrahman Tchiani suka tuntsurar da gwamnatin shugaba Muhammad Bazoum ne dai danganta ta yi tsami tsakanin Nijar da Najeriya, da kuma kasashen duniya da dama, ciki har da Amurka da na Turai, da kuma ita kanta Faransa, tsohuwar uwar gijiyarta.
Manya daga cikin dalilan juyin mulkin. kamar yadda gwamnatin mulkin sojin ta sanar a wancan lokaci sune cin hanci da rashawa, da kuma kasa shawo kan matsalar tsaro, abubuwar biyu da wasu masu sharhi ke ganin cewa ”Har yanzu shugaba Tchiani ya gaza shawo kansu, shi ya sa ma yake neman karkatar da hankalin al’ummar ƙasarsa, ta hanyar ɗorawa wasu laifi”
Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN
Koma dai menene a fili take cewa Nijar na da muhimmiyar rawar takawa ta fuskar yaƙi da matsalolin tsaro a yankin Sahel, musamman na ƙungiyoyin masu da’awar jihadi irin su Boko Haram da ISWAP, sai dai ana ganin shi kansa wannan na cikin barazana, duba da cewa kasar ta sa ƙafa ta fice daga ƙawancen ƙasashen da ke yaƙi da wannan matsala.
Yanzu dai Nijar ta rungumi Rasha, bayan fatattakar Amurka da kuma Faransa, kana akwai dakarun sojojin haya na ƙungiyar tsaro ta Wegner da dama a ƙasar da ke taimaka mata wajen yaki da matsalar tsaron.
Kana Nijar ta fice daga kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma wato ECOWAS, inda ta haɗa kai da sauran kasashen da sojoji suka kwace mulki da suka haɗa da Mali da Burkina Faso, suka kafa wata sabuwar kungiyar mai suna AES.