BUK Ta Daga Likkafar Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo zuwa Matsayin Farfesa

Date:

Daga Zakariyya Adam Jigirya

 

Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta amince da daga likkafar Dr. Sani Umar Rijiyar Lemo OON, zuwa matsayin Farfesa a fannin ilmin Hadisi a sashin ilimin addinin musulunci na Jami’ar .

Jaridar Kadaura24 ta rawaito cewa jami’ar ta amince da karin girman na Sheikh Sani Rijiyar Lemo a matsayin Farfesa a wata sanarwa da ta fitar a ranar 27 ga watan Disamba, 2024.

Dr. Sani Umar Rijiyar Lemo OON, malami ne a Jami’ar Bayero Kano shekaru da dama da suka gabata, ya yi digiri na biyu a babbar jami’ar Musulunci ta Madina.

Talla

Wani rubutu da aka tabbatar a shafin Facebook na Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo daga sashin Islama na Jami’ar Bayero Kano, ya sanar da karin girma a ranar Juma’a, yana mai cewa karin girma ya fara aiki daga Oktoba 2023.

Farfesa Rijiyar Lemo ya rubuta litattafai masu tarin yawa a matsayin gudummawar samar da ilimin addinin Musulunci da suka hada da Fayyatacec Bayani, tafsirin Alkur’ani da aka rubuta da harshen Hausa a shekarar 2020, Dhawābidhul Jarh wa Al-Ta’deel, Nabiyyur Rahmah, tarihin rayuwar Annabi. Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama.

Mutanen yankunan da Tchiani ya yi zargin an jibge sojojijn Faransa sun yi martani

Sauran su ne, Tamāmul Tawfeeq, tarihin Halifa na farko Abubakar al-Siddeeq (RA), Umarul Fāruq, tarihin Halifa Umar Al-Fāruq (RA) na Biyu, Labarin Ɗaluta da Jaluta, mai nuna tarihin Alƙur’ani mai girma. Ṭālūt (Saul) da Goliath, suna ɗaukar darasi a cikin shugabanci da siyasa.

Tuni dai makusantan malamin suke ta taya shi murnar samun wannan matsayi na Farfesa, cikinsu kuwa har da Farfado Mansur Sokoto wani sanannen Malamin Addinin Musulunci a Nigeria da sauran dalibai da masoyan malamin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...