Daga: Aliyu Danbala Gwarzo
Shugaban Kungiyar NNPP New Madia na jihar kano Comd. Salman Ibrahim Muhammad yace sun karrama shugaban karamar hukumar Gwarzo ne saboda kokarin da yake yi domin kawo cigaba ga al’ummar yankin.
Comd. Salman ya kara da cewa zasu cigaba da sanya idanu akan ayyukan da shugabannin kananan Hukumomi 44 daka jihar kano suke yi domin su basu lambar girmamawa wanda hakan na kara zaburar da shuwagabanin wajen cigaba da ayyukan Alkairi ga al’ummar da suke shugabanta.
Ya kuma ce shugaban karamar Hukumar Gwarzo shi ne na farko da su ka fara karramawa saboda tun yana shugaban riko yake aikace-aikacen bunkasa jama’a la’akari da hakan yasa suka fara da shi.
A nasa jawabin bayan karramashi a ofishinsa dake sakatariyar Gwarzon a ranar talata, shugaban karamar Hukumar Dr. Mani Tsoho ya bayyana farin cikinsa da wannan karramawa, tare da bayyana yadda suke fadi tashi wajen kawo cigaban da zai amfani al’umma ta fuskar ba da tallafin karatu ga Dalibai.
Kwankwaso ya taya Ganduje Murnar Cika shekaru 75
Ya kara da cewa wannan karamawa da aka yi masa tasa zai kara kaimi tare da shan alwashin cigaba da ayyuka daban-daban, kuma a shirye su ke su yi tafiya kafada da kafada da irin wadannan kungiyoyi domin kawo ciga a fadin jihar kano
Daga karshe ya yabawa gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa cormd Aminu Abdussalam Gwarzo a bisa yadda suke basu dama bisa yadda suke sahale musu idan suka kai koken wata matsala data addabi Alumma karamar Hukumar Gwarzo.