Kwankwaso ya taya Ganduje Murnar Cika shekaru 75

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Babban Daraktan harkokin Kuɗi na hukumar raya kogunan Hadejia -Jama’ar Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso ya taya Shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje murnar cikarsa shekaru 75 da haihuwa.

” Tabbas Dimokaradiyyar Nigeria zata dade tana amfana da irin gudunmawar da Ganduje ya bayar wajen dorewarta, don haka muke alfahari da shi”.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana hakan ne cikin Sakonsa na taya Ganduje murna wanda ya aikowa Kadaura24.

Talla

“A matsayinsa na shugaban jam’iyyarmu ta APC na ƙasa, Ganduje ya hada kan yan jam’iyyar a fadin ƙasar nan, wanda hakan yasa jam’iyyar take samun nasarori a zabukan cike gurbi da aka yi a ƙasar”. Inji Dr Musa Iliyasu

Babban Daraktan Kuɗi na hukumar raya kogunan Hadejia -Jama’ar ya ce a madadinsa da iyalansa da magoya bayansa yana taya Dr. Abdullahi Umar Ganduje murnar zagayowar ranar da aka haife shi.

Adadin Tafiye-tafiyen da Tinubu ya yi a shekarar 2024

” Muna addu’ar Allah ya kara masa lafiya da kwarin gwiwar cigaba da hidimtawa dimokaradiyyar Nigeria, da kuma ciyar da jam’iyyarmu ta APC gaba”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...