Sanata Barau ya taya Ganduje Murnar Cika shekaru 75

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Nigeriya, Sanata Barau I. Jibrin, ya taya Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, murnar cikarsa shekaru 75 da haihuwa, inda ya bayyana shi a matsayin gwarzon dimokaradiyyar Nigeria.

Kadaura24 ta rawaito Sanata Barau, a wani sako na musamman da ya aikewa tsohon gwamnan jihar Kano, mai dauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, ya bayyana cewa Ganduje yana shugabancin abun koyi kuma wanda suke alfahari da shi, saboda yadda ya samar da haɗin kai a tsakanin yan Jam’iyyar APC wanda hakan ne yasa suke samun nasara.

An haifi Dr. Ganduje ne a ranar 25 ga Disamba, 1949, don haka a wannan rana ta Laraba bikin cika shekaru 75 a duniya.

Talla

Ya ce a karkashin shugabancin Ganduje Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gudanar da zabuka 5 wadanda ba a yi a yayin babban zaɓen kasa ba, inda ya ce APC ta yi nasara lashe zabuka 4 cikin guda biyar da aka gudanar.

Sanata Barau Jibrin ya bayyana Ganduje a matsayin babban ginshikin dimokuradiyya a Nigeriya, Inda ya ce ba za a iya mantawa da irin gudunmawar da Ganduje ya bayar ba wajen ci gaban dimokaradiyya da Nigeria baki daya.

Sanata Barau Ya Zo Na Ɗaya Wajen Gabatar da Mafi Yawan Ƙudurori a Majalisar Dattawa

“Kamar yadda na yi hasashe a lokacin da ya zama shugaban jam’iyyar siyasa mafi girma a nahiyar Afirka a ranar 3 ga watan Agustan shekarar da ta gabata, kima da darajar jam’iyyar APC sai cigaba take da habaka a karkashin jagorancin Ganduje wanda kowa yake yaba masa, hakan tasa na kirawo shi da gwarzon dimokaradiyyar. A karkashinsa, mun ci hudu daga cikin zabuka biyar da aka yi, Mun samu nasara a jihohin Kogi da Imo da Edo da kuma Ondo”. Inji Sanata Barau

Sanata Barau Jibrin ya yi addu’ar Allah SWT ya kara masa shi lafiya, da kuma kwarin gwiwar tafiyar da al’amuran jam’iyyar APC har ta kai ga nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano,...

Za mu karawa Limamai, Ladanai da Na’ibansu alawus na wata-wata – Shugaban Karamar hukumar Dala

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Suraj...

Zargin kisa a R/Zakara: Gwamnatin Kano za ta kafa kwamiti – Waiya

Gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta gudanar da...