Rundunar ƴansanda ta ƙasa ta yi gargadin cewa daga yanzu duk wani dan sanda da aka samu yana aikat abubuwan da suka saba da doka zai fuskanci hukunci, ciki har da Kwamishinan ‘Yansanda na rundunar da kuma masu kula da shi.
Sufeto-Janar na ‘Yasanda na Najeriya, Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin dakatar da kama matasa ba bisa ka’ida ba da kuma tsare su a fadin kasar nan nan take.

Sufeto-Janar, wanda ke fuskantar suka kan yawan kama mutane ba tare da dalili ba, tsare su da kuma take hakkin bil’adama, ya kuma bayar da umarni cewa a dakatar da duba wayoyin mutane ba tare da izini ba nan take.
Wannan gargadi na cikin wata wasikar sanarwa daga hukumar ‘yan sanda da aka fitar ranar 13 ga Disamba, 2024, wacce aka aika wa dukkanin rundunonin jihohi, kuma PidomNigeria ta samu kwafi.
Yanzu-yanzu: Gwamnan Kano ya aike da suneyen wadanda zai nada Kwamishinoni ga Majalisar jihar
A cikin wasikar da Sashen Ayyuka na Hedikwatar Rundunar ya sanya hannu, shugabannin ‘yansanda sun bayyana cewa irin wadannan dabi’u na rashin bin doka da rashin adalci na kara bata sunan Hukumar ‘Yan Sandan Najeriya.
A cewar sakon, wadannan abubuwan da suka saba doka sun taka rawa wajen tayar da zanga-zangar #EndSARS, wacce ta haifar da asarar dukiya da rayuka a baya.