Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Majalisar dokokin jihar Kano,ta tabbatar da sunayen mutane bakwai da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin tantance don ya nada su a matsayin kwamishinoni kuma mambobin majalisar zartarwa ta jihar.
Kafin tabbatar da su, sai da mutanen bakwai suka kwace sama da sa’o’i uku da rabi, inda majalisar ta amincewa gwamnan ya nada su a matsayin kwamishinoni.

Kakakin majalisar Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore, ya bayyana cewa gwamnan ya sake aiko da Sunan Nura Iro Ma’aji domin tantance shi a matsayin kwamishina bayan wadancan sunaye na Mutane shida da aka fara tura sunayensu.
Ga sunayen wadanda Majalisar ta Amince da su:
Tsohon shugaban maβaikata: Shehu Wada Sagaji, wanda aka sauke shi daga mukaminsa a ranar Alhamis din da ta gabata.
Kotun Ζoli ta kori Ζarar da ke neman ta sauke Tinubu daga shuagaban Nigeria
1. Ambassador Ibrahim Waiya
2. Shehu Wada Sagagi
3. Abdulkadir Abdulsalam
4. Gaddafi Sani Shehu
5. Dr. Dahiru Hashim Muhammad
6. Dr. Ismail Aliyu Dannaraya
7. Nura Iro Ma’aji