Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya aikewa majalissar dokokin jihar wasika mai dauke da sunayen mutane 6 da yake son nadawa a matsayin kwamishinoni domin neman amincewa.
Idan za a iya tunawa a makon da ya wuce gwamnan ya yiwa majalisar zartarwarsa garanbawul tare da sallamar wasu daga cikin su.

Shugaban Majalisar Alhaji Jibril Ismail Falgore shi ne ya karanta wasikar a yayin zaman majalisar na yau.
Wadanda gwamnan ya aike da sunan su sun hadar
Na Yi Nadamar Abun da Na Yiwa Marigayi Nafi’u – Jarumar TikTok Babiana
1- Alh. Shehu Wada Sagagi
2- Alh. Abdulkadir Abdulsalam (AG)
3- Ibrahim A. Waiya
4- Dr. Isma’il Danmaraya
5- Dr Ghaddafi Sani Shehu
6- Dr. Dahir M. Hashim.
Majalissar ta bukace su, su bayyana a gaban ta a gobe talata da misalin karfe goma na safe domin tantance su.
Ga dai sunayen ma’aikatun da a yanzu haka ba su da kwamishinoni:
1.Rural
2.Finance
3. Environment
4. Information
5. Humanitarian Affairs.
6. Power.