Daga Rahama Umar Kwaru
Kungiyar matasa ta African Youth Assembly for Peace AYAP karkashin daraktan kungiyar na Nigeria Amb. Yakubu Hussain Takai ta karrama Sanata Shehu Buba a matsayin gwarzon Sanatan da yafi kowanne Sanata a yankin Arewa Maso gabashin Nigeria.
Shugaban kungiyar ya ce an baiwa Sanatan wannan lambar yabon ne duba da irin kokarin da yake yi wajen hada kan matasa da sanya su cikin harkokin mulki, lafiya da tsaro a jihar Bauchi da kasa baki daya.
Ga Kadan daga cikin tarihin Sanata Buba Shehu wanda shi ne yake wakiltar al’ummar Bauchi ta Kudu, An haifi Sanata Shehu Buba Umar a ranar 2 ga watan Oktoban shekarar 1979 a kauyen Nabordo dake karamar hukumar Toro ta jihar Bauchi.

Ya fara harkokin aikin gwamanti a matsayin Malamin makaranta kafin ya zama mataimaki na musamman, sannan ya kuma zama babban mataimaki na musamman a ofisoshi da dama a karkashin gwamnatin jihar Bauchi a lokacin gwamnatin Gwamna Isa Yuguda.
Haka kuma ya taba zama mai baiwa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar shawara na musamman. Sannan ya kuma jagoranci kwamitoci daban-daban da suka hada da kwamitin sasanta rikicin manoma da makiyaya, inda ya nuna jagoranci na gari ta hanyar jajircewarsa wajen magance matsalolin da suka addabi mazabarsa.
Da dumi-dumi : Shugaban ƙasa Tinubu zai yiwa al’ummar Nigeria jawabi
Sanata Buba Shehu a matsayinsa na Babban Darakta kamfanin Kasuwanci na Aquawave Oil and Gas, ya bayar da gudunmawa sosai wajen habaka fannin mai da iskar gas, inda ya samar da guraben aikin yi ga ‘yan Najeriya da dama musamman matasa.
A wata Sanarwa da sakataren kungiyar AYAP mai kula da Arewa ta tsakiya, Umar Ahmad Ladan ya ce Daraktan kungiyar na ƙasar nan sun Karrama sanatan ne da lambar yabo mafi girma saboda gudunnawar da Sanata Umar yake bayarwa don cigaban matasan yankinsa da Nigeria baki daya.
“Wannan karramawar dai wata sheda ce da ke nuna irin nasarorin da ya samu da kuma sadaukar da kai ga aikin gwamnati. Yallabai, muna fatan za ku ci gaba da bayar da gudunmawar ku wajen ci gaban jihar Bauchi, da shiyyar Arewa maso Gabas, da kuma Nijeriya baki daya”. Inji Daraktan kungiyar Yakubu Hussaini Takai
Sanarwar ta kuma taya Sanata Umar Buba Shehu murnar samun wannan lambar yabo, ya yin da kuma aka yi kira ga sauran Sanatocin Arewacin Nigeria da su yi koyi da Sanata Buba Shehu saboda irin gudunnawar da yake bayarwa don cigaban matasa.