Daga Kamal Yahaya Zakaria
Dalibin siyasar duniya, kuma mai sharhi kan al’amuran siyasar Nigeriya Alhaji Bashir Hayatu Gentile, ya bukaci shugaban majalisar wakilan Nigeria Tajudeen Abbas da ya ji tsoron Allah kar ya bari a cutar da al’ummar Arewacin Nigeria, ta hanyar amince da kudirin dokar gyaran haraji da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aika musu.
“Ka sani Allah ne ya baka wannan mukamin da ka ke kai ba Tinubu ko jam’iyyar APC ba, kuma ka tuna kai Dan gidan sarautar Iyan Zazzau ne, don haka kar ka bari ayi amfani da mukamin da Allah ya baka har a zo da wani abu da zai cutar da al’ummar Arewacin Nigeria”.
Bashir Gentile ya bayyana hakan ne cikin wani sakon Murya da ya aikowa Jaridar KADAURA24 a ranar Juma’a.
Ya ce kudirin harajin da Tinubu ya tura majalisa, idan har ya sami amincewa yan majalisar zai cutar da al’ummar Arewacin Nigeria sosai, don haka ya ce shugaban majalisar ya yiwa Allah da manzonsa Kar ya bari kudirin ya wuce.
” Na tattauna da yan majalisar tarayya na arewa sun kai 187 Amma dukkaninsu sun tabbatar min da cewa kai ne matsala domin ka hura musu wuta sai sun baka goyon bayan kan tabbatar da wannan kudiri na haraji da zai lalata rayuwar wadanda ma ba a haifesu ba, domin zai lalata komai na Arewacin Nigeria”. Inji Bashir Gentile
“Ina kara yi maka nasiha mai girma iyan Zazzau ka ji tsoron Allah, domin Allah ya ce duk abun da ka shuka shi zaka jirba walau alheri ko akasin haka, don haka kar ka bari ayi amfani da kai wajen bautar da al’ummar Arewacin Nigeria”.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito al’umma da dama Arewacin Nigeria suna ta sukar wannan kudirin gyaran dokar harajin, wanda masa suka ce zai gurgunta tattalin arzikin Arewacin Nigeria baki daya.