Yanzu-Yanzu: An kashe Dan ta’addan da ya shirya Sace Daliban Makarantar Kankara ta jihar Katsina

Date:

Rahotonni sun tabbatar da cewa fitaccen dan ta’addan da ya shirya sace ‘Yan Makarantar Kankara a cikin jihar Katsina, Auwalun Daudawa an kashe shi.
 Wannan na zuwa kwanaki kadan bayan ya koma daji.


 Kwamishanan tsaron harkokin cikin gida na jihar Zamfara, Abubakar Justice Dauran ne ya tabbatar wa DW Hausa da labarin.


 Daily Trust ta ruwaito cewa an kashe Daudawa ne da yammacin ranar Juma’a a lokacin da sukai musayar wuta da wasu gungun abokan hamayyarsu a dajin Dumburum da ke tsakanin karamar Hukumar Zurmi a Jihar Zamfara da karamar Hukumar Batsari a Jihar Katsina.


 Shahararren dan fashin nan ya yi kaurin suna bayan da ya kitsa kai hari a Makarantun Sakandaren Gwamnati da ke Kankara inda ya sace sama da ’yan makaranta 300 a cikin dare.
 Watanni biyu bayan haka, dan fashin ya bayyana a Gusau, babban birnin Zamfara, tare da mutanensa biyar inda ya sanar da tubansa tare da mika bindigogin AK guda 20 da wasu makamai ga ‘yan sanda.

2 COMMENTS

  1. Lallai Kadaura na bayar da gagarumar gudunmawa ga makaranta Hausa a Jafar sadarwa zamani.
    Allah ya taimaki Kadaura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gidauniyar Pyramid of Heart sun kai tallafin na’urar Oxygen Concentrated Asibitin Murtala dake Kano

Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhd dake Kano ya yabawa...

Da dumi-dumi: ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta fara

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta dakatar da...

Ba mu da wata matsala da Ofishin mataimakin shugaban Kasa – NAHCON

Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta karyata wani rahoto...

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nemi hukumar NBC ta fadada aikinta kan kafafen yada labarai na intanet

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci Hukumar...