‘Yan majalisar NNPP sun amince da tsige Ali Madaki tare da bayyana wanda zai maye gurbinsa a mukaminsa na majalisa

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

‘Yan majalisar wakilai 15 cikin 18 da aka zaba a jam’iyyar NNPP, sun amince da tsige dan majalisa mai karamar hukumar Dala, Ali Madaki, a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar.

A cikin wata takarda da jaridar DAILY NIGERIAN ta gani a ranar Litinin, ‘yan majalisar da ba su saka hannu a takardar neman cire Madakin ba, su ne mambobin Dala, Rano/Kibiya/Bunkure da Karaye/Rogo — Ali Madaki, Kabiru Alhassan Rurum da Abdullahi Sani Rogo.

A cikin wata wasika da aka aike wa kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, tare da hadin gwiwar shugaban jam’iyyar NNPP da sakataren jam’iyyar NNPP Ajuji Ahmed da Dipo Olayoku, sun bukaci a tsige Madakin gini a maye gurbinsa da dan majalisa mai wakiltar Dawakin Tofa, Rimin Gado Tofa Tijjani Abdulkadir Jobe.

Talla

“Mun rubuta wannan wasika ne domin mika sunan babban dan jam’iyyarmu, HON TIJJANI ABDULKADIR JOBE domin maye gurbin Hon Aliyu Sani Madaki a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar. A cewar wasikar

Rikicin NNPP: Na hannun daman Kawu Sumaila Anas Abba Dala ya bayyana matsayarsa

“Muna fatan za ku gaggauta daukar wannan mataki da muka nema a cikin wannan wasikar bisa la’akari da muhimmancinsa ga jam’iyyarmu, da majalisar baki daya .

Duk da cewa ba a bayar da dalilin tsige Madakin gini ba, jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa Madaki a kwanakin baya ya yi watsi da tafiyar Kwankwasiyya, kuma ya yi mubaya’a tsagin jam’iyyar NNPP mai kayan marmari ta Boniface Aniebonam.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...