Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kano kan harkokin siyasa Alhaji Anas Abba Dala ya bayyana cewa Babu wata baraka tsakanin gwamnan jihar kano da Sanatan Kano ta Kudu Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila.
“Mutane sun kasa fahimtar cewa babu wata rashin fahimta da ta ke faruwa tsakanin gwamnan Kano da Sanata Kawu Sumaila, duk abun da ake gani Siyasa ce kawai, amma suna girmama junansu sabanin yadda mutane suke gani”.
Alhaji Anas Abba Dala ya bayyana hakan ne lokacin wata ganawa da yayi da jaridar Kadaura24 a ranar asabar .

Alhaji Anas Abba Dala wanda makusanci ne ga Sanata Kawu Sumaila tun da jimawa, ya ce wasu mutane ne kawai suke kokarin ganin sun rura wutar rikicin Amma, ya ce ba za su nasara ba.
Ƙanin Kwankwaso ya maka Gwamna Abba Gida-Gida a Kotu akan Batun Fili
” Ni bana kaunar ganin an yi Rikici a wannan gwamnatin ta mu, amma Ina so duniya ta sani ni matsayata ita ce Ina tare da gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf kuma wallahi idan kuri’a ta ita kadai ce ta rage zan baiwa Gwamna Abba don ya cigaba da mulkin Kano”. Inji Anas Abba Dala
Idan za’a iya kadaura24 ta rawaito an sami rashin jituwa tsakanin gwamnatin jihar kano da Sanatan Kano ta Kudu Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila.