Za mu tabbatar da umarnin gwamnan Kano na haramta bayar da filaye Barkatai – Kwamishinan Kasa

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Kwamishinan ma’aikatar filaye da tsare-tsare ta jihar Abduljabbar Muhammad Umar ya bukaci ma’aikatan ma’aikatarsa ​​da su tashi tsaye wajen gudanar da ayyukansu tare da kula da ka’idoji aikinsu yadda ya dace.

A Wata sanarwa da daraktan wayar da kan al’umma na ma’aikatar Umar Abdu Kurawa ya aikowa kadaura24, yace Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin da ya zagaya ma’aikatar don ganin irin gyare-gyaran da Ake gudanarwa a cikin ma’aikatar.

Talla

Ya ce ya zama wajibi ma’aikatan su kara kaimi wajen gudanar da aikinsu, domin hakan zai taimaka wajen inganta aiyukan ma’aikatar domin amfanin al’ummar jihar Kano.

Ya jinjinawa Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa himma da kishinsa na samar da yanayi mai gamsarwa ga ma’aikatan Ma’aikatar tare da nuna jin dadinsa da yadda aikin ke gudana cikin gaggawa.

Yadda Shekarau ya ƙwace fulotin da ya bayar domin gina makarantar Islamiyya a Kano

Sannan ya umarci dan kwangilar da ke aikin da ya tabbatar da kammala aikin a kan lokaci kamar yadda ya yi alkawari domin ma’aikatan ma’aikatar su rika gudanar da aikinsu cikin sauki.

“Idan an kammala aikin cikin gaggawa Ma’aikata za su iya komawa ofishinsu na dindindin kuma su ci gaba da yin aiki tukuru domin jin dadin jama’a a jihar”.

Alh. Abduljabbar ya kara da cewa, Gwamnatin Abba Kabir Yusuf a halin yanzu ba za ta lamunci mummunan halin da ake na rabon fili barkatai a lungu da sako na jihar ba kamar yadda ya sanya hannu akan dokar haramta bayar da filaye Barkatai.

Kwamishinan ya kuma yi kira ga jama’ar jihar kano da su baiwa gwamnatin Abba Kabir Yusuf hadin kai don inganta rayuwarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...