Daga Isa Ahmad Getso
Kwamishinan ma’aikatar filaye da tsare-tsare ta jihar Abduljabbar Muhammad Umar ya bukaci ma’aikatan ma’aikatarsa da su tashi tsaye wajen gudanar da ayyukansu tare da kula da ka’idoji aikinsu yadda ya dace.
A Wata sanarwa da daraktan wayar da kan al’umma na ma’aikatar Umar Abdu Kurawa ya aikowa kadaura24, yace Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin da ya zagaya ma’aikatar don ganin irin gyare-gyaran da Ake gudanarwa a cikin ma’aikatar.

Ya ce ya zama wajibi ma’aikatan su kara kaimi wajen gudanar da aikinsu, domin hakan zai taimaka wajen inganta aiyukan ma’aikatar domin amfanin al’ummar jihar Kano.
Ya jinjinawa Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa himma da kishinsa na samar da yanayi mai gamsarwa ga ma’aikatan Ma’aikatar tare da nuna jin dadinsa da yadda aikin ke gudana cikin gaggawa.
Yadda Shekarau ya ƙwace fulotin da ya bayar domin gina makarantar Islamiyya a Kano
Sannan ya umarci dan kwangilar da ke aikin da ya tabbatar da kammala aikin a kan lokaci kamar yadda ya yi alkawari domin ma’aikatan ma’aikatar su rika gudanar da aikinsu cikin sauki.
“Idan an kammala aikin cikin gaggawa Ma’aikata za su iya komawa ofishinsu na dindindin kuma su ci gaba da yin aiki tukuru domin jin dadin jama’a a jihar”.
Alh. Abduljabbar ya kara da cewa, Gwamnatin Abba Kabir Yusuf a halin yanzu ba za ta lamunci mummunan halin da ake na rabon fili barkatai a lungu da sako na jihar ba kamar yadda ya sanya hannu akan dokar haramta bayar da filaye Barkatai.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga jama’ar jihar kano da su baiwa gwamnatin Abba Kabir Yusuf hadin kai don inganta rayuwarsu.