NNPP Ta Lashe Zaɓen Ƙananan Hukumomin Kano Baki Ɗaya

Date:

 

 

Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, ta lashe kujerun shugabancin ƙananan hukumomi 44 da kansiloli 484 a zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a ranar Asabar.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC) ce, ta ayyana jam’iyyar a matsayin wadda ta lashe zaɓen gaba ɗaya.

Talla

Shugaban KANSIEC, Farfesa Sani Lawan Malunfashi ne, ya sanar da hakan da yammacin ranar Asabar.

Ya bayyana cewa KANSIEC ta gudanar da aikinta na gudanar zaɓen ƙananan hukumomi a Jihar Kano.

A cewarsa, an gudanar da zaɓen cikin lumana da nasara.

Za mu hada kai da sabbin Shugabannin kananan hukumomi don ciyar da Kano gaba – Gwamna Abba

Ya gode wa hukumomin tsaro, kafofin yaɗa labarai, shugabannin jam’iyyu da al’umma, tare da ƙungiyoyin matasa da mata da suka bayar da goyon baya ga tsarin dimokuraɗiyya.

Ya kuma mika godiyarsa ga mutanen Jihar Kano bisa goyon bayansu na tabbatar da zaɓen ya gudana cikin lumana.

Jam’iyyu shida ne suka shiga zaɓen na ranar Asabar; AA, AAC, Accord, ADC, APM, da kuma jamiyyar NNPP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano za ta fara jiyo ra’ayoyin al’umma kafin gudanar da duk wani aiki a jihar – Bilkisu Indabo

Daga Samira Hassan   Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin nan...

Kwankwaso ya gana da Tinubu a fadar shugaban kasa

Daga Nasiba Rabi'u Yusuf   Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso,...

Neman Ilimin addini dana boko da sana’a ba kishiyoyin juna ba ne – Dr. Aminu Sagagi ga matasan Zango

Daga Rahama Umar Kwaru   Wani Malamin addinin musulunci a kano...