Janar Gawon ya fadi yadda akai masa juyin mulki da makusantansa da aka hada baki da su

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Tsohon shugaban Najeriya a zamanin mulkin Soja Janar Yakubu Gowon dake bikin cika shekaru 90 a duniya ranar asabar, ya ce ya sami labarin cewar za ayi masa juyin mulki daga hukumomin tsaronsa tun kafin ayi kuma sunayen mutanen da aka gabatar masa na manyan jami’ansa ne da suka fito daga jiharsa ta Benue-Filato ta wancan lokaci.

Gowon ya bayyana sunayen kwamandan dakarun dake tsaron fadar shugaban kasa da suka hadar da Joe Garba da Tony Ochefu, amma sai ya ki amincewa da rahotan ganin saboda sun fito ne daga jiharsa, kana kuma dukkansu Kiristoci ne.

Janar Gowon ya ce ya yi kokarin ji daga Ochefu amma bai iya kai wa gare shi ba, ya yin da shi kuma Joe Garba ya yi ta rantsuwar cewar babu wani abu mai kama da haka.

Talla

Tsohon shugaban ya bayyana mutanen 2 a matsayin masu kima a wurinsa saboda yadda suka taimaka masa wajen tabbatar da Najeriya ta kasance kasa guda.

Gowon ya ce a lokacin sai bukatar tafiya taron shugabannin kasashen Afirka ta taso, kuma shi ke matsawa takwarorinsa a kan su daina kauracewa taron, saboda haka ya tafi Kampala dake kasar Uganda tare da kwamishinan yan sanda Farouk Usman, kuma a wajen taron shugaban Uganda na lokacin Idi Amin ya shaida masa cewar an kifar da gwamnatinsa.

Talla

Yakubu Gawon dai ya mulki Nigeriya daga ranar 1 ga watan Ugusta na Shekarar 1966 zuwa ranar 29 ga watan juli na Shekarar 1975 Daily Trust

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...