Daga Kamal Yahaya Zakaria
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf a madadin gwamnatin jihar Kano ya sanar da bayar da tallafin Naira Miliyan Dari ga wadanda gobara ta shafi shagunansu a cikin shahararriyar kasuwar Kantin Kwari a kwanakin baya.
Gwamnan ya sanar da bayar da tallafin ne a lokacin da ya jagoranci manyan jami’an gwamnati Inda suka je kasuwar domin yiwa yan kasuwar jaje a ranar alhamis.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24 , ya ce gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna kaduwarsa Kan Iftila’in da ya sami yan kasuwar ta kwari.
Gwamnan ya ce tallafin ba diyya ba ne ga asarar da aka yi Sanadiyar a gobarar, a’a, an bada shi ne domin rage radadin ga wadanda gobara ta yiwa barna.
Sabon Rikici ya balle tsakanin yan majalisar tarayya na jam’iyyar NNPP a Kano
Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bada tabbacin gwamnatin jihar Kano zata inganta yanayin kasuwar domin samun yanayi mai kyau da saukin kasuwanci a kasuwa ta hanyar sanya fitulu masu amfani da hasken rana; gyaran hanyoyin cikin kasuwar, gina magudanun ruwa da samar da rijiyoyin burtsatse da sauran su.
Ya roki shugabannin kasuwar da su bullo da shirye-shiryen da za su taimaka wa dubun dubatar ’yan kasuwar don gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da tangarda ba tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta yi duk abin da ya dace domin Kano ta ci gaba da rike matsayinta na cibiyar kasuwanci a Arewacin Najeriya wasu kasashen yammacin Afirka.

Tun da farko, Manajan Daraktan Hukumar Kula da Kasuwar Kantin Kwari, Alhaji Hamisu Sa’ad Dogon Nama ya ce shaguna 29 ne gobarar ta kone, kuma ya yaba da yadda jami’an kashe gobara da sauran masu ruwa da tsaki suka yi gaggawar daukar matakin dakile yaduwar gobarar .
Shugaban Kwamitin Dattawan Kasuwa, Alhaji Sabu’u Bako ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa yadda ya nuna damuwa da halin da ‘yan kasuwar ke ciki, ya kuma yi kira ga Gwamnan da ya taimaka wajen magance wasu matsalolin da ke kawo cikas a kasuwar.