Sabon Rikici ya balle tsakanin yan majalisar tarayya na jam’iyyar NNPP a Kano

Date:

Daga Sani Idris Maiwaya

 

Rikici ya barke tsakanin ‘yan Kwankwasiyya na jam’iyyar NNPP, yayin da wata zazzafar muhawara ta barke tsakanin ‘yan majalisar wakilai, Aliyu Sani Madaki, da Abdulmumini Jibrin Kofa.

Aliyu Sani Madakin gini dai a yanzu shi ne dan majalisar tarayya mai wakilar karamar hukumar Dala , shi kuma Abdulmumini Jibril Kofa shi ne dan majalisar tarayya mai wakilar kananan hukumomin Kiru da Bebeji Kuma dukkaninsu yan Jam’iyyar NNPP ne daga jihar kano.

A wasu rubuce-rubuce da madakin gini ya yi a sashin shafinsa na Facebook ranar alhamis, ya ce zai tonawa Abdulmumini Jibrin kofa asiri.

Talla

“Salamu alaikum.

Jama’ar jihar Kano dama kasa baki daya, yau zan gaya muku,wane ne Abdulmumini Jibrin wane Aliyu Sani Madaki.Tunda bashi da kunya to yau zan fadi waye shi da kuma me yayi mun da Kwankwaso da abunda da ya fada mun akan kwankwaso.

Jama’a ina zuwa ajira kadan”. A cewar Madakin gini

Waɗannan kalamai dai sun sanya al’umma da dama shakku game da zaman lafiyar jam’iyyar ta NNPP, saboda ana ganin a ranar larabar da ta gabata ne gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jagoranci wani zama da yan majalisun a Abuja domin kawo daidaito a jam’iyyar.

Da dumi-dumi: Jarumi Adam A Zango ya sami Mukami

Jim kadan bayan wadancan kalamai an sake ganin Madakin gini ya sake wallafa hoton Kofa da sunayen wasu yan majalisar da a yanzu basu cikin majalisar, amma dai masu biyayya ne ga tsagin Kwankwasiyya ko a wancan lokacin, sannan ya yi wani rubutu kamar haka:

*Jama’a zan baku labarin wannan hoton da dalilin yinsa don ku gane waye Hon Abdulmumin Jibrin” . Inji Madakin gini

Yadda Gwamna Yusuf ya tasamma warware rikicin cikin gida da ya taso a NNPP Kano

Hoton takardar da Madakin gini ya sanya tana dauke ne da sa hannun wasu fitattun ‘yan siyasa irin su Nasiru Sule Garo, Hon. Sani Muhammad Rano, da Hon. Ado Damburam Abubakar Nuhu, da dai sauransu.

Talla

Wannan rikicin na zuwa ne biyo bayan rikicin cikin gida na ake zargin ya kunnu kai tsakanin Sanata Kawu Sumaila, da yan Jam’iyyar NNPP, wanda a baya-bayan nan ya musanta zarge-zargen da ake yi masa musamman gane da zaben 2023, lamarin da ya kara tayar da hankulan jama’a a cikin jam’iyyar NNPP.

Da Majiyar KADAURA24 ta Solacebase tuntubi mai magana da yawun Abdulmumini Jibrin Kofa, dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Bbebji da Kiru, Sani Paki akan batun, cewa ya yi shugaban nasa zai mayar da martani a daidai lokacin da Aliyu Sani Madaki, dan majalisa mai wakiltar mazabar Dala ya tona asirin da ya sha alwashin tonawa.

Za Mu cigaba da bibiyar wannan lamari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...