Nigeria@64:Matsalolin Nigeriya na bukatar dabaru wajen magance su – Gwamnan Kano

Date:

 

 

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce Najeriya na fuskantar manyan matsaloli da dama da ke buƙatar dabaru domin magance su.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Kano da su kasance masu kishin ƙasa domin tabbatar da samun gobe mai kyau.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24, yace Gwamna Yusuf ya yi wannan kira ne a lokacin bikin cikar Najeriya shekaru 64 da samun ‘yancin kai da aka yi a filin wasa na Sani Abacha da ke jihar.

Talla

Gwamnan ya ce, “Yayin da muke tunawa da gudummawar shugabanninmu na baya, ya kamata mu yi tunanin abin da za mu iya yi don ci gaban wannan jiha mai girma. Ta yaya za mu tabbatar da cewa hidimar da iyayenmu suka yi ba ta tafi a banza ba? Mu yi fatan alheri, haɗin kai, da kuma tafiya a kan manufa guda ɗaya.

“Mu koyi darasi daga nasarorinmu na baya da ƙalubalen da muka fuskanta, mu fuskanci rayuwar gaba da jarumta. Tare, za mu iya shawo kan kowace irin matsala, mu cimma burinmu, kuma mu ciyar da ƙasar nan gaba.

Yancin kai: Muhimman bangarori 6 na jawabin shugaban ƙasa Bola Tinubu

“A yau, a bayyane yake cewa muna fuskantar matsaloli da dama. Daga matsalolin tattalin arziƙi zuwa rashin daidaito a zamantakewa, batun tsaro har zuwa tasirin sauyin yanayi, muna fuskantar ƙalubale da ke buƙatar hanyoyi masu ƙarfi da ƙirƙire-ƙirƙire.

“Duk da haka, ba za mu bari waɗannan matsaloli su dakatar da mu daga ƙoƙarin gina kyakkyawar makoma ga kowa a Jihar Kano da Najeriya ba.”

Gwamna Yusuf, ya kuma yi fatan samun kyakkyawar makoma, sai dai ya jaddada cewa hakan zai dogara ne da yadda mutane za su haɗa kai, kamar yadda shugabanni baya suka yi.

“Dole ne mu haɗa kai ba tare da la’akari da bambance-bambancen siyasa, ƙabilanci, da addini ba don fuskantar manyan matsalolin da muke fuskanta.

Talla

“Kowannenmu yana da rawar da zai taka, ko kai shugaba ne na gargajiya, shugaba na addini, ma’aikacin gwamnati, manomi, malami, dalibi, ko ɗan kasuwa.

“Ta hanyar aiki tare, bayar da gudunmawa ga al’ummarmu, da kuma bibiyar shugabanni kan abin da suka yi, za mu tabbatar da cewa an samar da ƙasa mai ƙarfi, daidaito, da kuma tsayuwa fiyw da yamma muka same ta.”

Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da mayar da hankali kan aiwatar da ayyukan da za su amfani al’umma da kuma bunƙasa jihar.

“Za mu ci gaba da yin aiki tuƙuru don inganta rayuwar mutanenmu, haɓaka ci gaban kowa da kowa, da kuma gina al’umma inda kowa zai iya cika burinsa kuma ya bayar da gudunmawa mai tasiri ga ci gabanmu baki ɗaya,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...