Yadda al’ummar Kano suka ki amsa kiran masu zanga-zangar tsadar rayuwa

Date:

Daga Sani Idris Maiwaya

 

Al’ummar jihar Kano sun yi watsi da zanga-zangar tsadar rayuwa da masu fafutuka suka shirya yinta a wanan rana ta 1 ga watan October a duk fadin Nigeria.

Wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, wanda ya kewaya cikin birnin Kanon, ya ruwaito mazauna garin suna ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata matsala ba.

Talla

Titunan sun kasance cikin kwanciyar hankali, kasuwanni da manya da kananan shagunan duk sun bude suna ta gudanar da harkokin kasuwancinau kamar yadda aka saba, su kuma jami’an tsaro na sintiri don dakile duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya a jihar.

Alhaji Isa Musa wani mazaunin unguwar Dakata da ke karamar hukumar Nasarawa, ya ce zanga-zangar ba ta da amfani, duba da kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na magance bukatun kungiyoyin kwadago.

Nigeria@64: Yan Nigeriya za su yi alfahari da ƙasarsu a karkashin gwamnatin Tinubu -Minista T Gwarzo

“Mun fi damuwa mu nemi abincin da zamu kaiwa Iyalanmu fiye da zanga-zangar da ba zata haifar da komai ba,” in ji Musa.

Yancin kai: Muhimman bangarori 6 na jawabin shugaban ƙasa Bola Tinubu

A nasa bangaren, wani Musa Abubakar daga Farm Centre a karamar hukumar Tarauni, ya ce da yawa daga cikin mazauna yankin ba su san da wannan zanga-zangar ba, domin kasuwancin su suke yi kamar yadda aka saba.

Shi kuwa Malam Abubakar Muhammad mazaunin Unguwar Kofar Wambai na karamar hukumar birni, ya yabawa gwamnatin jihar kan matakan inganta rayuwar al’ummar Kano.

Talla

Muhammad ya kuma yabawa jami’an tsaro kan matakan da suka dauka na wanzar da zaman lafiya a birnin.

NAN ta ruwaito cewa Dorayi, Dukawuya, Kabuga, Rijiyar Zaki, Naibabawa da sabon Titi sun kasance cikin kwanciyar hankali.(NAN).

Sai dai kadaura24 ta sami labarin yanzu haka ana gudanar da zanga-zangar a babban birnin tarayya Abuja da jihar Lagos.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...