Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Waɗanda suka yi mining din Hamster Kombat sun koka matuka bisa yadda farashinsa ya fito babu daraja a ranar farko da ya fara shiga kasuwar cikifto.
Idan za a iya tunawa tun watanni 6 da suka gabata Matasa da dama a duniya suka fara harkar mining din Hamster Kombat da tunanin zai yi daraja a kasuwa.

A yau alhamis 26 ga watan Satumba da misalin karfe 1 na rana ne dai Hamster ya fashe wanda hakan yake nuna cewa ya shiga kasuwa domin yin hada-hadar shi a kasuwar Kirifto.
Gwamnatin Kano ta ciyo bashin makudan kudade don inganta ruwan sha
Hamster Kombat dai ya fito kowanne daya akan 0.01 wanda hakan ya fusata yan baiwa ma’ana waɗanda suka yi mining din Hamster Kombat.

Da yawa daga cikin wadanda suka fara mining daga kan Hamster Kombat dai sun yanke kauna tare da yin alkawarin daina yin duk wani mining.
A gefe guda kuwa wadanda suka dade suna harkar mining sun ce yanzu ma suka fara, har suna karawa sabbin yan baiwa kwarin gwiwar cigaba da mining din.