Sanya Haraji mai yawa akan taba sigari ne kadai hanyar magance shan ta – CISLAC

Date:

Daga Abubakar Yakubu

 

Wata kungiya mai zaman kanta dake rajin samar da dokokin da zasu taimaka wajen cigaban al’umma mai suna Civil Society Lagislative Advocacy center (CISLAC) ta bukaci gwamnatocin jihohin Nigeria da yi dokokin da zasu kara yawan harajin da suke karba akan kamfanonin taba sigari domin rage yawan masu shanta don inganta rayuwar al’ummarsu.

” Daga lokacin da aka kara kudin harajin taba sigari dole masu kamfanonin za su kara kudin siyanta, hakan zai sa yawan masu siyanta ya ragu ko ma wasu su daina baki daya”.

Talla

Shugaban kungiyar CISLAC na ƙasa Auwal Ibrahim Musa Rafsan Jani ne ya bayyana hakan lokacin wani taron karawa juna sani da kungiyar ta shiryawa masu zuwa da tsaki a harkar.

Ya ce akwai bukatar masu ruwa da tsaki kan batun musamman wadanda suka hadar da ma’aikatar lafiya, muhalli da ta Kuɗi da su tsara yadda gwamnatocinsu zasu samar da dokar kara kudin haraji ga taba sigari don rage illar da take yiwa al’umma.

Gwamnatin Kano ta ciyo bashin makudan kudade don inganta ruwan sha

” Akwai cututtuka da dama suke kama masu shan taba sigari wadanda kuma suna hallaka mutane, sannan hayakinta yana gurbata muhalli da kuma kashe kudade”. Inji Rafsanajani

Yace bayan gwamnatin tarayya ta yi nata kokarin suma gwamnatocin jihohi suna da gagarumar rawar da zasu taka wajen ganin an rage yawan shan taba sigari saboda illar da take da ita ga rayuwar al’umma da muhalli da kuma tattalin arzikin kasa.

Talla

” Kara kudaden harajin zai rage yawan shan tabar saboda masu kamfanonin zasu kara kudinta, Sannan gwamnati za ta sami kudaden shiga da zata iya yin amfani da su wajen gudanar da aiyukan raya kasa da cigaban al’ummarsu.

Masana daban-daban ne suka gabatar da makaloli a yayin taron da aka gudanar jihar kano dake Arewa maso yammacin Nigeria.

Muhalarta taron dai sun fito ne daga jihohin Kano Jigawa Katsina Bauchi da jihar Gombe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...