Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Kungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya, PENGASSAN, ta yi karin haske kan dalilan da suka sanya manya dillalan man fetur a Nigeria ke kasa sayen man fetur kai tsaye daga matatar Dangote.
Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban kungiyar Festas Osifo a wani taron manema labarai a Legas a ranar Talata, ya ce lamarin ya samo asali ne daga sabanin farashin da aka samu tsakanin kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) da kuma farashin da yake sayarwa ga ‘yan kasuwa masu zaman kansu.

Osifo ya bayyana cewa kamfanin na NNPC na iya siyan man akan N950, amma ya sayar wa ‘yan kasuwa masu zaman kansu akan kusan N700, wanda hakan zai haifar da gagarumin gibi da NNPC ke cikewa.
Ya ce idan manyan ‘yan kasuwa za su sayi man kai tsaye daga matatar Dangote to zasu saye shi ne akan farashi irin daya da yadda NNPCPL take siya, ka ga dole za su bukaci a sayar da shi a kan farashi mai yawa, mai yuwuwa sama da N1,000.
Yan sa-kai sun hallaka Ƙasurgumin dan ta’adda a jihar Zamfara
‘Yan kasuwa masu zaman kansu sun gwammace su sayi man daga NNPCPL don cin gajiyar rahusar da kamfanin yake yi musu, in ji shi.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito an sha yin dambarwa tsakanin kamfanin man fetur na Nigeria NNPC da Matatar Ɗangote kan yadda farashin man zai Kasance, daga karshe dai kamfanin na NNPP ya fara siyan man fetur na matatar Ɗangote a ranar 15 ga wannan watan na Satumba akan farashin naira 898.