Wani Jirgin Sama da ya bata da fasinjoji kusan 300 yan Nigeria a sauka a Kano

Date:

Wani jirgin sama mallakar Saudi Airlines na ƙasar saudiyya ya da ya ɓace da fasinjoji kusan 300 ƴan Najeriya ya sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, bayan shafe sama da awanni 10 da tasowarsa.

Freedom Radio ta rawaito Jirgin ƙirar Boeing 777-300 mai lamba SV 0401 ya taso daga filin jirgin sama na Sarki Abdul’aziz da ke Jidda da misalin ƙarfe 10 da rabi na safiyar ranar wanda ake sa ran zai sauka Kano da ƙarfe 2 na rana, amma hakan bai samu ba.

Talla

Bayan awanni 3 da tashin jirgin ne, sai ya ɓace daga manhajar da ake bibiyar zirga-zirgar jiragen sama, lamarin da ya jefa iyalai da ƴan uwan fasinjojin cikin zullumi.

Dalilin da ya sa ‘yan kasuwar mai a Nigeria suka gwammace sayan man a NNPCL maimakon matatar Dangote – PENGASSAN

To sai dai jirgin ya samu sauka a Kano da ƙarfe 8:30 na daren Talata.

Jami’an jirgin sun sanarwa da fasinjoji cewa, jirgin ya sauka ne a Habasha domin rashin lafiya wani daga fasinjoji.

Talla

Sai dai wasu fasinjojin da Freedom Radio ta tuntuba sun ce, jirgin lalacewa yayi domin a inda aka sauke su, an shafe awanni biyar Injiniyoyi na ta aiki a kansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...