Daga Badiya Muhd
Masu kallo su na tsaka da shaukin kallon shirin fim mai dogon zango na Kwana Casa’in, kwatsam aka wayi gari daya daga cikin jaruman shirin fim Rahma Mk din ta yi aure.
Binciken da kadaura24 ta gudanar sun tabbatar da auren jarumar ,wanda aka daura safiyar ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamban 2021.
Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, an yi shagalin bikin ne a gidan su da ke birnin Kano a sirrance don ba a bayyana wa mutane da dama ba.
Rahma Mk wadda ita ke fitowa a matsayin matar Bawa mai kada tsohon gwamnan jihar Alfawa a cikin shirin na kwana chasa’in.
Rahotanni sun nuna yadda aka yi shagalin bikin a gidan su da ke cikin garin Kano cike da sirri don ba kowa ya sani ba.
Tuntuni an samu labari a kan batun auren jarumar amma ba ta fadi lokaci da kuma wanda za ta aura ba, hakan ya sa mutane su ka dinga mamaki.
Yayin da manema labarai sun bukaci jin ta bakin jarumar,inda ɗ ta bayyana cewa:
“Dama na shaida cewa zan yi aure tun kwana 3 da su ka gabata, kuma ga shi Allah ya tabbatar kuma ya cika min buri na.”
Ta kara da addu’ar Allah ya ba ta haihuwa kuma ta yi fatan mutuwa a dakin mijin ta.
Batun fina-finai kuma ta ce za ta ci gaba da fitowa a shirin Kwana Casa’in, amma sauran babu tabbas.