Budaddiyar Wasika Zuwa ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu
Ya mai girma shugaban kasa,
Dangane da murabus din da kakakin shugaban kasa Ajuri Ngelale ya yi bisa dalilin radin kansa a baya bayan nan, akwai matukar bukatar a cike wannan gurbin mukami da mutumin da ya iya aiki da kwarewa.
A ra’ayina na, babu wanda ya fi dacewa da cike wancan gurbi da ya wuce Abdulaziz Abdulaziz, mai taimaka maka na musamman kan harkokin yada labarai na yanzu, mutum ne mai hazaka da gogewa, da kwazo. Abdulaziz yana da kwarewa da gogewar da zai iya rike wannan mukami domin kare muhibba da kimar wannan gwamnati ta ka.
A tarihinsa dan jarida ne da ya fara aiki tun daga mai dauko rahoto har zuwa matakin edita, inda ya yi aiki a manyan jaridu irin su Blueprint, Premium Times, da Daily Trust, ya bar tarihi mai kyau da ya ke ci gaba da yawo a fadin Najeriya.
Abdulaziz ya sami lambobin yabo da dama da suka hada da babbar lambar yabo ta Wole Soyinka Center for Investigative Journalism Award. Mutuncin sadaukarsa da kimarsa abar alfahari ne da koyi duk da kasancewarsa kusa da masu mulki a cikin Aso Rock Villa. Bashi da girman kai, kuma har yanzu yana da kyakyawar ala da abokansa da abukan mu’amalarsa a harkar yada labarai.
Zaɓen 2027: Kwankwaso Ya Bugi Kirji
Duk da kalubalen da yake cikin kare gwamnati mai ci, musamman idan aka yi la’akari da manufofin tattalin arziki da suka jawo wa ‘yan Najeriya da dama wahala, Abdulaziz yana ci gaba da aiki tukuru tare da jajircewa wajen fadakar da jama’a kokarin gwamnatin. Ya tunatar da ’yan Najeriya cewa nan gaba za a fita daga cikin mawuyacin halin da ake ciki. Yana amfani da ƙwarewarsa a fannin yada labarai wajen gudanar da aikinsa cikin hikima .
Ba a iya kwarewar aiki kadai Abdulaziz yake da ita ba, a kashin kasan yana da kyawawan halaye na mu’amalanta kowa Inda ya mayar da abokansa tamkar yan uwansa na jini.n san shi ba kawai don gwanintarsa ba har ma da halayensa na kashin kansa. Wadannan halaye na sa suna kara masa daraja a wajen mutane da dama, a ciki da wajen masana’antar yada labarai.
Karin Farashin Man Fetur da VAT Zai Karawa Yan Nigeria Matsin Rayuwa -Atiku ga Tinubu
Nada Abdulaziz Abdulaziz a matsayin mai magana da yawun shugaban kasa zai yi kyau sosai, domin zai yi amfani da kwarewa wajen kare muhibbar gwamnatinka . Shahararsa, musamman a yankin Arewacin kasar nan inda ya fito, zai kara habaka alaka da gwamnatin ku da yankuna daban-daban.
A matsayina na dan Najeriya kuma mai sharhi kan al’umma, ina rokonka, mai girma shugaban kasa, da masu girma a makusantan shugaban kasaz da ku baiwa wannan shawara tawa kulawa ta musamman . Abdulaziz Abdulaziz ya fi cancanta da mukamin.
Na ba da wannan shawarar ne ba a matsayin aboki ba kawai, saboda yakinin cewa Abdulaziz Abdulaziz shi ne mutumin da ya fi cancanta ya gaji Ajuri Ngelale a matsayin kakakin shugaban kasa .
Na gode,
Nasiru Zango
7 ga Satumba, 2024.