Karin Farashin Man Fetur da VAT Zai Karawa Yan Nigeria Matsin Rayuwa -Atiku ga Tinubu

Date:

Daga Hafsat Abdullahi Muhammad

 

Tsohon mataimakin shugaban kasar Nigeria Atiku Abubakar ya kalubalanci shirin da gwamnatin tarayya ke yi na kara haraji na VAT wato (Value Added Tax).

Atiku ya ce manufar za ta kara matsalar tsadar rayuwa ga yan Nigeria da kuma kara tabarbara ci gaban tattalin arzikin Najeriya .

A wata sanarwa da Atiku ya fitar ranar Lahadi ta shafinsa na X, ya ce matakin na iya ta’azzara lamarin halin kunci da al’umma suke ciki.”

Zaɓen 2027: Kwankwaso Ya Bugi Kirji

Ya kara da cewa, matakin kara farashin man fetur da kamfanin man fetur na Najeriya NNPC ya yi, zai karawa sanya yan Nigeria cikin mawuyacin hali tare da kara gurgunta tattalin arzikin kasar da dama yake cikin wani hali.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, ya ce babu bukatar sai mutum ya zama masani kan tattalin arziki kafin ya fahimci illar da manufofin Shugaba Tinubu suka yi wa tattalin arzikin Najeriya da makomar yan ƙasar.

ya kara da cewa da Shugaban kasar zai zai yi kyan kai da mai da hankali wajen farfado da tattalin arzikin Nigeria maimakon kara dagula lamuran da suka shafi cigaban tattalin arzikin kasar dana yan ƙasar baki daya .

Yanzu-yanzu: Gwamnatin Kano ta dage ranar komawa da makarantu

Ya ce, “Ƙara VAT zai kara rura wutar matsin rayuwar da al’umma suke ciki, abun takaici shi ne yayin da mutane suke wahala shi kuma (Tinubu) yana siyan sabbin jiragen sama da motoci don kansa da iyalansa.

“Shugaba Bola Tinubu, tare da jiga-jigan masu ba shi shawara, sun kuduri aniyar kara kudin harajin VAT daga kashi 7.5 zuwa kashi 10 cikin 100, duk da cewa kamfanin NNPC ta sanar da karin farashin kuɗin man fetur.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...