Jam’iyyar adawa ta APC a jihar Kano ta nuna fatan Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila ya dawo gidan sa na siyasa da ya bari.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Sanata Sumaila ya fice daga APC ne a gabanin zaɓen 2023, inda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa (a wancan lokacin) ta NNPP kuma ya tsaya takara a nan har ya ci zaɓe.
Karin Farashin Man Fetur da VAT Zai Karawa Yan Nigeria Matsin Rayuwa -Atiku ga Tinubu
Sai dai kuma a yayin kaddamar da rabon kayan abinci da shugaban kasa ya bayar a rabawa talakawa a Kano a yau Lahadi, kakakin jam’iyyar APC a Kano, Ahmed Aruwa, ya yi fatan Kawu Sumaila ya dawo jam’iyyar ta su.
Yayin da ya ke yi mika sannu da zuwa ga manyan baki da su ka halarci taron, Aruwa, cikin barkwanci ya ce “Sanata Kawu Sumaila, Sanatan alheri. Allah Ya maida koko masaki. Allah Ya dawo mana da kai jam’iyyar APC,”
Zaɓen 2027: Kwankwaso Ya Bugi Kirji
Bayan da Aruwa ya fadi wannan kalamai, sai gurin ya rude da shewa da cewa “ameen”.
Sai dai kuma Daily Nigerian Hausa ta gano cewa Aruwa ya baiyana wannan fata ne a kashin kan sa ba da yawun jam’iyyar APC ba.