Zaɓen NAWOJ: Yan jaridu a Kano sun bayyana gamsuwa da yadda kwamitin zabe ke aikin sa

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Wasu Yan Jaridu Mata a Kano sun yaba da yadda kwamitin zaben shugabannin kungiyar mata yan jaridu NAWOJ suke gudanar da aikinsu.

A Wata sanarwa mai dauke da sa hannun wasu mata 12 wadda suka aikowa kadaura24, sun ce sun rubuta wasikar ne domin yabawa da namijin kokarin da kwamitin ke yi don ganin ya shirya sahihi kuma ingantaccen zabe.

” Babu shakka Mun gamsu da yadda kuke gudanar da aikinku kuma hakan ya ba mu kwarin gwiwar cewa za ku yi adalci yayin zaben ba tare da saukar wani bangare ba”.

Talla
Talla

Sanarwar ta ce kwamitin ya na gudanar da aikinsa bisa gaskiya da Adalci da kuma nuna ƙwarewa yayin daukar kowanne irin mataki.

” Muna yaba mu ku bisa yadda kuka rage kudin sayen fom na takarar kowacce kujera, wanda hakan ke nuna cewa kun yi la’akari da halin matsin tattalin arziki da Ake fama da shi a duk fadin Nigeria”.
Dear Credentials Committee:

An Karrama Mai Magana Da Yawun Gwamnan Kano Kan Batun Taimakawa Daliban Dawaki Tofa

Ga jerin sunayen wadanda suka sanyawa sanarwar hannu

Aisha Ibrahim Malami
Hassana Aminu
Aysha Musa Ilyas.
Umma Abdul
Maryam Tata
Zulaiha Ahmad
Halima Muhammad
Habiba Sabo Abubakar
Binta Kabir
Ummi Muhamma
Maryam Galadanci
Aisha Kabara

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...