Gwamna Yusuf ya nemi haɗin kan gidauniyar Qatar don magance matsalolin da ke damun mutanen Kano

Date:

Daga Sani Idris Maiwaya

 

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nemi tallafin gidauniyar Qatar Charity domin bunkasa kokarin da ya ke yi na tunkarar kalubalen da ke addabar al’umma musamman ta fuskar samar da ruwa, gidaje, ilimi, da inganta harkokin mata.

Gwamnan ya yi wannan roko ne a wata ziyarar aiki da ya kai ofishin Qatar Charity da ke Abuja, kamar yadda mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24 a ranar Alhamis.

Gwamnan ya jaddada bukatar hada kai domin fadada ayyukan samar da ruwan sha mai tsafta a jihar, inda ya ce tuni aka samar da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana, tare da shirin kara wasu ayyuka nan da watanni masu zuwa.

Babban Hadimin Gwamnan Kano ya ajiye Mukaminsa tare da Komawa APC

Sai dai ana bukatar karin tallafi domin magance matsalar karancin ruwa da ke addabar al’umma da dama a Kano.

Bugu da kari, gwamnatin jihar Kano tana kuma neman taimakon Qatar Charity wajen gina gidaje a filayen da gwamnati ta bayar domin samar da matsugunni ga marasa galihu da suka hada da marayu da sauransu.

Gwamnan ya kuma bayar da shawarar samar da wata cibiya mai amfani ga al’umma a cikin wadannan rukunnen gidaje, wanda zai zama cibiyar harkokin ilimi, sana’a, da zamantakewa.

Sace takardun Shari’a : Ganduje ya yiwa gwamnatin Kano martani

Gwamnan ya kuma yi kira da gidauniyar da ta tallafa wa musu karamin karfi da tallafin karatu ta yadda za su samu ilimi mai inganci.

Gwamna Yusuf ya amince da irin gagarumar gudunmawar da Qatar Charity ta bayar a wasu ayyuka a fadin Najeriya, da suka hada da daukar nauyin marayu, ayyukan kula da ido, gina masallatai da samar da ruwa.

An ƙayyade kuɗin fom din tsayawa takara a zaɓen ƙananan hukumomin Kano

A nasa jawabin, Daraktan Gidauniyar Elsayed Mohamed Abdou Hamdi ya yabawa Gwamna Yusuf, bisa matakin da ya dauka da ba a taba yin irinsa ba na ziyartar ofishin su domin amfanin al’ummar Kano.

Ya kuma mika godiyarsa ga gwamnan jihar kan yadda ya samar masu da hanyar taimakawa mazauna Kano sabanin gwamnatocin da suka gabata.

Don haka ya ba da tabbacin cewa za su ba da dukkan goyon bayan da suka dace don ganin al’ummar Kano sun ci gajiyar kokarinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...