Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Jami’ar Najeriya ta farko da ke da salon karatun Burtaniya da Faransa, Jami’ar Franco-British International University, Kaduna, za ta fara harkokin koyo da koyarwa a watan Oktoba 2024.
Shugaban jami’ar Farfesa Abdullahi Muhammad Sabo ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin.
A cewar shugaban jami’ar, jami’ar za ta fara ne da koyar da harkokin Komfuta, (School of Computer) da koyar da harkokin aikin jinya, ( School of Nursing) da kuma harkokin Kimiyyar Lafiya (School of Health Sciences).
Dan Bello ya sanya wa jam’iyyar APCn Kano sharadin dakatar da yi mata bankade-bankade
Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, shi ne ya kafa jami’ar ta Franco-British International, wanda kuma shi ne mamallakin Jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria da wadda ke Nijar da kuma Jami’ar Canada ta Najeriya da ke Abuja.
A wata sanarwa da ya fitar a lokaci da shugaban jami’ar tarayya ta Dutsin-Ma ya ziyarce shi, Farfesa Armayau Hamisu Bichi, Farfesa Gwarzo ya nanata kudirin na kishin harkokin ilimi, inda ya bayyana cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen cigaba da bunkasa fannin Ilimi.
“Kafa Jami’ar Franco-British International University (FBI) wani yunƙuri ne na samar da ingantaccen ilimi a Afirka,” in ji shi.
Yadda aka sace Naira biliyan 50 daga asusun Gwamnatin Kano
Hukumar kula da jami’o’i ta Nigeria ta baiwa Jami’ar Franco-British International lasisin aiki na wucin gadi a shekarar 2023, tare da Jami’ar Canada ta Najeriya, wacce kuma ke cikin rukunin jami’o’in MAAUN.
“An san ni da ilimi kuma zan ci gaba da jajircewa akan hakan. Mun yi hakan ne a Nijar da Kano, inda muka cusa son ilimi da bin ka’idojinsa a tsakanin dalibanmu da ma’aikatanmu.
Za mu tabbatar da hakan a tsakanin ɗalibai da ma’aikatan Jami’ar Franco-British International University, kamar yadda muke yi a Kano da Nijar,” in ji Farfesa Gwarzo.