Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana damuwarsa kan rikicin sarauta da ke faruwa a jihar Kano, inda ya jaddada cewa duk da halin da ake ciki na damunsa, amma ya zabi kada ya tsoma baki cikin lamarin.
Da yake jawabi a wani shirin Siyasa na gidan talabijin din Channels TV, Shekarau ya danganta rikicin da siyasa tare da bayyana fatan ganin an magance matsalar cikin gaggawa.
Malam Shekarau, wanda shi ne Sardaunan Kano ya ce shi ya fi damuwa da zaman lafiyar jihar Kano da kwanciyar hankalinta.
Zargin karkatar da shinkafa: APC ta yi barazanar daukar matakin shari’a kan jami’an gwamnatin Kano
Ya bayyana cewa matakin da ya dauka na kin sa baki a kan lamarin ne tun lokacin da ya sami labarin batun ya je gaban kotu .
“Ni babban dan majalisar sarki ne, kuma baya ga haka, na yi mulkin jihar, don haka ni dattijo ne a jihar , shi yasa tun ranar da na ji an kai maganar kotu, na ce ba zan ce komai akan maganar ba,” in ji Shekarau.
Shekarau ya bayyana cewa shigar da ‘yan siyasa suka yi cikin lamarin shi ne babban abin da ya kara ta’azzara rikicin masarautun, yana mai nuni da cewa masarautun gargajiya za su iya tafiyar da lamarin yadda ya kamata idan aka bar su suna gudanar da harkokinsu na kansu.
Kama sojan da ya harbe matashi a Zariya abun a yaba ne — Atiku
Ya kuma jaddada mahimmancin hadin kai tsakanin sarakuna da jami’an gwamnati domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.
“Yan siyasa ne duk suka haifar da wannan rikicin, kuma da ace ’yan siyasa suna nisantar da duk irin wannan, kuma ba sarakuna an ba su cikakkiyar damar tafiyar da al’amuransu, tabbatar da ba a sami irin wannan matsalar ba,” inji Shekarau. “Sarakuna shugabannin al’umma ne, kuma gwamna da wadanda ya nada su ma shugabannin al’umma ne, don haka dole a sami fahimtar junan tsakanin su don cigaban al’ummar su.”
Da ya waiwayi lokacin da ya rike gwamnan jihar Kano, Shekarau ya ce a lokaci ya hada kai da Sarkin Kano wajen bujiro da wasu ayyuka na cigaba al’umma, domin nuna yadda sarakuna da gwamnati za su hada kai domin ci gaban al’ummar da suke jagoranta.