Hukumar Kwastam ta Najeriya, ta buƙaci masu zanga-zangar yunwa da su yi tsammanin samun ragin farashin kayayyakin abinci na ba da jimawa ba.
Kwanturola-Janar na hukumar, Bashir Adewale Adeniyi ne, ya bayyana hakan a hedikwatar tsaro da ke Abuja a ranar Talata.
Adeniyi, yana cikin shugabannin tsaro da suka halarci taron sirri wanda babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya kira.
Atiku ya gargadi hafsoshin tsaron Nigeria kan harbin masu zanga-zanga
Daily trust ta ruwaito cewa a ranar 1 ga watan Agusta ne dubban ‘yan Najeriya suka gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar kan tsadar rayuwa.
“Shigowa da kaya daga waje yana ɗaukar lokaci. Don haka ɗaya daga cikin abubuwan da shugaban ƙasa ya yi na rage tasirin farashin shigo da kaya shi ne dakatar da harajin Kwastam da haraji kan kayan abinci da ake shigowa da su na wani lokaci.
“Mun yi imanin cewa idan aka aiwatar da hakan, zai taimaka wajen rage farashin kayayyakin abinci a kasuwanni. Hukumar Kwastam ta Najeriya ta himmatu wajen aiwatar da wannan manufa.”
Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron, shugaban hukumar ta Kwastam ya ce za a yi wa wasu kayan abinci da ake shigowa da su rangwame ba tare da karɓar harajin ba domin karya farashinsu.