Atiku ya gargadi hafsoshin tsaron Nigeria kan harbin masu zanga-zanga

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya gargadi hafsoshin tsaron Nigeria da kwamandojin soji a kan ba da izinin amfani da muggan makamai a kan masu zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a fadin Nigeria .

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata, Atiku ya ce za a daurawa shugabannin tsaro alhakin harbin fararen hula masu zanga-zangar lumana da sojoji da sauran jami’an tsaro suke yi.

Talla
Talla

Ya rubuta: “Ina so in yi tsattsauran gargaɗi ga manyan hafsoshin tsaro da kwamandojin sojan Najeriya, musamman waɗanda suke ba da izinin yin amfani da bindiga wajen harbin masu zanga-zangar lumana, su sani cewa su za a tuhuma da aikata laifuffukan cin zarafin bil adama, ko da bayan sun yi ritaya daga aiki.”

Bayan koken al’ummar Kano, shugabannin Singa sun ce yan kasuwar su ji tsoron Allah

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi kira ga hukumomin tsaron da su tabbatar da baiwa masu zanga-zangar kariya, domin abun da suke yi dokar kasa ce ta ba su damar yi.

“Hakkin da ya rataya a wuyan gwamnati da hukumomin tsaro ne su tabbatar da tsaro da kariya ga mutanen da ke su ka yar da zasu nemi ‘yancinsu ta hanyar gudanar da zanga-zangar lumana.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...