Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta ce ta kama wani malamin makarantar Islamiyya bisa zargin sace dan dan uwansa domin karbar kudin fansa.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba ta hannun kakakinta, SP Gambo Isah, rundunar ta ce ta kama malamin mai suna Jamilu Idris da ke karamar hukumar Faskari bisa zargin sace dan dan uwansa, Umar Farouk Kabir, dan shekara hudu.
A cewarta, ranar 9 ga watan jiya Jamilu ya je gidan dan uwansa, Kabiru Abdullahi a Funtua ya sace dansa zuwa garin Dutsen-Alhaji da ke Abuja, babban birnin kasar.
BBC Hausa ta rawaito Rundunar ta ce daga nan ne Jamilu ya kira yayan nasa ya bukaci ya bayar da kudin fansa da suka kai naira miliyan biyar.
Ta kara da cewa mutumin ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa.