Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24 da ta sanya a jihar a jiya na tsawon sa’o’i 5.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa gwamnan jihar kano,Abba Kabir Yusuf ya sanya dokar hana fita a ranar Alhamis bayan zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa ta rikide zuwa tashin hankali wanda ya kai ga rasa rayuka da sace-sace.

Gwamnan ya ce an sassauta doka daga 12 na rana zuwa karfe 5 na yamma domin baiwa mutane damar zuwa sallah Juma’a.
Da yake magana a madadin gwamnatin Kano Kwamishinan Shari’a na jihar Barr. Haruna Isa Dederi gwamnati ba zata lamunci karya dokar da ta sanya ba.