Cikin Shekara guda Na Sami Nasarar daga darajar Kano Poly – Dr Kabiru Dungurawa

Date:

Daga Musa Mudi Dawakin Tofa.
Shugaban kwalejin Kimiyya da fasha ta jihar Kano Dr Dungurawa ya cika shekara daya a kujerar sa.
Dr Kabir Bello Dungurawa ya karbi shugabancin Kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kano wato Rector Kano state Polytechnic daga hannu Farfesa Mukthar Atiku Kurawa kuma ya shiga ofis  Ranar 2 ga watan Nuwamba, 2020.
Kazalika, Ranar 2 ga watan Nuwamba, 2021 ita ce Ranar da Rector Dr Kabir Dungurawa ya cika shekara daya cur a kan mulkin gudanarwar Kwalejin.
Idan har za a iya tinawa Dr Dungurawa a Ranar da ya shiga ofis ya bayyana wasu manufofi bakwai wato (seven point Agenda) da yake fatan cimmawa a lokacin Shugabancin nasa.
A zantawar sa da wakilin Kadaura24 Shugaban Kwalejin yace izuwa Ranar da ya cika shekara daya ya samar da kwamitoci biyar zuwa shida tun lokaci da ya shiya ofis don ganin ya dabaka manufofin nasa, daga ciki  ya ce ya biya duk kudaden alawus ga ma’aikatan wucin gadi kuma yana biyansu 25 ga kowanne wata, Sannan a cikin shekera daya malamai 46 ya baiwa da damar karo karatu zuwa matakin karatun digiri na biyu dana a uku a ciki da wajen kasar nan a karkashin asusun bada tallafin na kasa, ya ciyar da malamai 125 zuwa matakin albashi na gaba, domin dalibai su samu sukunin karatu ya gyara dakin karatu a kwalejin aka ya kuma sanyawa  dakin karatun suna Farfesa Hafsa Abdullahi.
Dr. Dungurawa, ya ce sun samar da karin kwamfutoci a reshensu dake karamar hukumar Rano don shirin tinkarar fara zana jarabawar JAMB ta kwamfuta wato CBT doraya akan guda daya da kwalejin tuni ta samar, yace ya samar da karin sabbin kwasa-kwasai 9 wanda  Kwalejin zata fara nan gaba da zarar an gama tantancesu. a bangaren samar da haske don kara inganta tsaro a kwalejin Dr Kabiru Dungurawa yace ya samar da fitulu 25 masu amfani da hasken rana tare da biyan kaso 60 cikin 100 na bashi kudin wutar lantarki da suka gada ga Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na Kano wato KEDCO.
A bangaren wasannin don kara samar da nishadi a tsakanin dalibai sun cigaba da dorawa a kan daukar dawainiyar gudanar da gasar  wasannin kwallo  mai suna Directors Cup da Rectors Cup.
Dr Kabir Bello Dungurawa ya samar da karin motoci biyu daga Gwamnan Kano Ganduje doriya a kan man Deisel da Gwamnan ke kawo don kara inganta ayyuka a kwalejin da sauransu.
Yace Kuma Zai cigaba da zage damtse don tabbatar da Kwalejin ta darar ma takwarorinta na fadin kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...