Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Wasu daga cikin masu zanga-zangar nuna adawa da wahalhalun da ake fama da su a fadin Nigeria, sun fara kona tayoyi a kofar gidan gwamnatin jihar Kano a safiyar ranar Alhamis.
Masu zanga-zangar da su ka fito daga sassa daban-daban na birnin Kano sun yi dandazo ne a gidan gwamnati, inda gwamna Abba Kabir Yusuf zai yi musu jawabi.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar ne suka hada tayoyi, kuma suka banka musu wuta a lokacin da suke tunkarar kofar.
Hakan ya sanya jami’an tsaron da ke gidan gwamnati suka harba bindiga sama da barkonan tsohuwa domin tarwatsa masu zanga-zangar.
Hakan tasa masu zanga-zangar suka rika guduwa zuwa wurare daban-daban .
Sai dai zuwa yanzu abubuwa sun daidaita domin jami’an tsaro su yi nasarar hana kona tayoyin , Inda suka bukaci masu zanga-zangar da su gudanar da zanga-zangar cikin lumana.