Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP), Kayode Egbetokun, ya umurci manyan jami’an ‘yan sanda da su kare wadanda suka shirya zanga-zangar da zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi mata take da #EndBadGovernance wadda aka shirya gudanarwa a ranakun 1 zuwa 10 ga Agusta, 2024.
Hakan na kunshe ne a cikin wasikar mayar da martani da babban sufeton ya aike wa lauyan nan mai kare hakkin dan Adam Ebun-Olu Adegboruwa.
Idan za a iya kadaura24 ta rawaito Adegboruwa, Babban Lauyan Najeriya (SAN), a ranar 26 ga Yuli, 2024, ya rubuta wa IGP wasikar neman a baiwa masu zanga-zangar kariya a yayin da zasu gudanar da ita.
Sufeto janar din, a cikin wasikar da mayar wa da lauyan martani mai dauke da kwanan wata 29 ga Yuli, 2024, ya umurci manyan jami’an ‘yan sanda da su saurari bukatar babban lauyan.
Tinubu ya dauki matakin da zai kawo karshen dambarwar Matatar Ɗangote da gwamnatin tarayya
Egbetokun ya mayar da martani ne a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun babban jami’in ma’aikatan sa, CP Johnson Adenola.
Sufeto janar din ya kuma bukaci ganawa da Adegboruwa a Abuja a ranar Talata, 30 ga watan Yuli, 2024, domin a ci gaba da tattaunawa kan bukatarsa.