Tinubu ya sa hannu kan dokar mafi ƙarancin albashi ta naira 70,000

Date:

 

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sa hannu kan dokar mafi ƙarancin albashi ta naira dubu 70,000.

Matakin ya kawo ƙarshen watannin da aka shafe ana tattaunawa tsakanin hukumomi da ƴan ƙwadago da kuma ɓangaren masu kamfanoni.

Tinubu ya sa hannu kan dokar a fadarsa da ke Abuja kwanaki bayan da majalisar dokokin ƙasar ta miƙa masa ƙudirin.

Talla
Talla

Mai bai wa shugaban Najeriyar shawara ta musamman kan al’amuran majalisar dattijai, Sanata Basheer Lado ne ya tabbatar da matakin cikin sanarwar da ya fitar a Abuja.

Ya ce sa hannu kan dokar da shugaba Tinubu ya yi na nuna ya cika alƙawarin da ya yi wa ƴan Nigeria musamman ma’aikata.

Rarara ya Magantu AKan Goge Shafinsa da Facebook Ya Yi

“A yaƙin zaɓe, Tinubu ya yi alƙawarin inganta rayuwar ma’aikata kuma ya cika alƙawarin” in ji Lado.

Bai tsaya iya nan ba, ya tabbatar cewa an samar da dokar mafi ƙanƙantar albashi da yanzu ya zama dole a yi nazafin mafi ƙankantar albashin duk bayan shekara uku saɓanin shekara biyar.

Matakin dai ya zo ne yayin da wasu al’ummar Najeriya ke shirin gudanar da zanga-zanga don nuna takaicinsu kan tsadar rayuwa da taɓarɓarewar tattalin arziki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...