Farfesa Gwarzo Ya Kalubalanci Jami’o’i Masu Zaman Kansu Kan Nagartar Ilimi

Date:

Daga Zainab Muhd Kabara

Shugaba kuma wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN) da kuma Franco-British International University (FBI-U), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya bukaci daukacin Jami’o’i masu zaman kansu da su mai da hankali kan daidaito da inganta ilimi da nufin kare nagartar ilimin a jami’o’i masu zaman kansu a Afirka da duniya baki daya.

Farfesa Gwarzo ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da takarda a matsayin babban bako mai jawabi a wajen taron yaye dalibai karo na 8 na Jami’ar IHERIS ta Togo da aka gudanar a ranar 30 ga watan Oktoba, 2021 a birnin Lome na kasar Togo tare da gabatar da ita ga manema labarai a Kano.

Farfesa Gwarzo wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Jami’o’in masu zaman kansu ta Afrika (AAPU), ya bayar da shawarar a samar da dabarun da za su kare Jami’o’i masu zaman kansu daga cibiyoyin gwamnati, musamman ma masu son kai, domin a cewarsa Jami’o’i masu zaman kansu suna kawo abubuwan ci gaba da yawa da ya hada da bunkasa harkar ilimi, wanda hakan ke samar da ƙarin buƙatun aiki da kuma damarmaki.

Farfesa Gwarzo ya bayyana Cewa dalibai suna sa ran Jami’o’i za su samar da ingantacciyar koyarwa tare da horaswa domin taimaka musu wajen cimma burinsu na ayyuka; a yayin da mutane masu ilimi kuma suke tsammanin Jami’o’i za su zama matakalar hawa wajen samun ingantaccen ilimi; ya kara da cewa, hukumomi da cibiyoyin gwamnati daidai gwargwado suna son Jami’o’i su kara taka rawa wajen tallafawa ci gaba da kuma bunkasa tattalin arziki baki daya.

Wanda ya kirkiro Jami’ar ta MAAUN din wanda ya gabatar da takarda a wajen kayataccen taron mai taken “TASIRIN HADIN KAI A TSAKANIN JAMI’O’IN AFIRKA MASU ZAMAN KANSU” ya bayyana cewa al’umma ta yi imanin cewa Jami’o’i za su iya taimaka mata wajen magance yawancin matsalolinta; kuma masana’antu suna da sha’awar Jami’o’i domin haka bayar da ingantaccen ilimi baa bin wasa ba ne a don haka dole ne a kiyaye shi.

Farfesa Gwarzo ya yi nuni da cewa, a wannan zamani da ake ciki na dunkulewar duniya da ‘yancin kai, yana da matukar muhimmanci a jawo hankulan jama’a, tare da tallatawa, da kuma karfafa samar da jami’o’i masu zaman kansu masu nagarta, da kuma fitar da wasu dokoki wanda za a kafa hanyar tallafawa jami’o’i masu zaman kansu a Afirka da kudade domin bayar da gudunmuwa ga ci gaban koyarwa da bincike a jami’a masu zaman kansu.

A cewar Farfesa Gwarzo, “Saboda saurin ci gaba da ake samu da kuma ganin jami’o’in sun karbu, bukatuwar samar da ingantattun ilimi a manyan makarantu yana karuwa a sakamakon gasa. Matsin da ake yi wa shugabannin jami’a domin su inganta hanyar koyarwa, binciken ilimi, da sauran ayyukan ilimi da ke da alaƙa yana haifar da su.

A cewar Farfesa Gwarzo, muhimmin abin da ke da nasaba da samar da ingantattun jami’o’i masu zaman kansu ba zai zama ya yi yawa ba duba da yadda yawan al’ummar Afirka ke karuwa bisa ga ma’aunin lissafi, ilimi, aikin yi, tattalin arziki da duk hanyoyin rayuwa suna karuwa a bisa lissafi wanda bai zama abin damuwa ba.

“Dangane da haka, ƙalubale da shawarwari; dole ne shugabannin gwamnatocin ƙasashe masu hankali na Afirka su mai da hankali sosai tare da taimakawa duka biyun ta fuskar aiwatar da manufofi masu kyau da kudade domin tabbatar da gaskiya, kafawa, aiki da dorewar jami’o’i masu zaman kansu tare da Cibiyoyin ilimi, duk da kasancewarsu ginshikan ilimi, haka kuma tare da samar da guraben aikin yi ga al’ummarmu tare da yawan matasa da ba su da aikin yi sai dai su tsunduma cikin ayyukan ta’addanci daban-daban, musamman shaye-shayen miyagun kwayoyi, tada kayar baya da kuma laifuka”, Farfesa Gwarzo.

An bai wa Farfesa Gwarzo lambar yabo ta ‘Shugabancin Afirka na shekaru goma’, saboda gudummawar da yake bayar wa daban-daban wajen daukaka darajar ilimi da inganta ilimin a Afirka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...