Gwamnatin jihar Kano ta ce ana samun karuwar masu rajistar zabe a jihar sakamakon fahimtar da al`umma ke yi game da muhimmancin zabe.
Gwamnatin jihar Kanon ta kafa wani kwamiti na musamman wanda ya shiga shelar wayar da kan al`umma, bayan ta gano cewa mutane da dama na dari-dari da yin rajistar zabe.
An kafa kwamitin wayar da kan masu zabe ne a jihar bayan rahotanni sun nuna cewa a jihohi da dama a Najeriya ciki har da Kanon, akwai tarin katunan zabe jibge a ofisoshin hukumar zabe, wadanda ke neman yin kwantai saboda masu katunan basu je sun karba ba.
Hakama akwai wadanda katunan su suka bata, ko suka lalace, da kuma wadanda suka cancanci kada kuri`a masu yawan gaske da basu je an yi musu rajistar ba.
BBC Hausa ta rawaito a cewar mataimakin shugaban kwamitin kuma kwamishinan raya karkara Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso, babban burin gwamnati dai shi ne kare matsayin jihar Kanon na rumbun kuri`a.
Ya kara da cewa ” abunda suke gani a zahiri na nuna cewa kwalliya na biyan kudin sabulu “.
A babban zaben 2019 jihar Kano ce tazo ta biyu wajen yawan masu kada kuri`a a fadin Najeriya da mutum sama da miliyan biyar, inda ta zo bayan jihar Legas mai mutum fiye da miliyan shida.